logo

HAUSA

Sama da jahohin Amurka 20 sun samu bullar sabon nau’in Omicron

2021-12-11 16:40:49 CMG

Sama da jahohin Amurka 20 sun samu bullar sabon nau’in Omicron_fororder_1211-U.S.-Omicron-Ahmad

Sabon rahoton da cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Amurka CDC ta fitar ranar Juma’a ya nuna cewa, a kalla jahohi 22 na kasar Amurka an samu rahoton bullar nau’in cutar COVID-19 ta Omicron, wanda ya hada har da wasu unguwanni da suka nuna alamun yaduwar cutar.

Daga cikin mutane 43 da aka fara bibiyarsu, an kwantar da mutum guda a asibiti, kuma babu rahoton wanda ya mutu, a cewar hukumar CDC.

Galibin alamomin da ake samu na masu kamuwa da sabon nau’in cutar sun hada da tari, kasala, da shakewar makoshi ko kuma yoyon hanci.

Bincike mafi yawa da aka gudanar sun nuna cewa, yawanci rahoton kamuwa da cutar yana da alaka da tafiye-tafiye na cikin gida da na kasashen waje, da halartar wuraren gangamin jama’a, da kuma yaduwar cutar a tsakanin magidanta.

Hukumar CDC tace, dabarun kandagarkin da ake amfani dasu a halin yanzu, sun hada da yin riga-kafi, amfani da takunkumin rufe fuska, samar da isassun hanyoyin samun iska, yin gwaji, da killace mutane na daga cikin hanyoyin da aka tabbatar suna rage yaduwar nau’in cutar SARS-CoV-2, wanda ya hada har da sauran nau’ikan cutar kamar Omicron, da kuma samar da kariya don kaucewa fuskantar tsananin cutar ko kuma hasarar rayuka daga cutar ta COVID-19.(Ahmad)

Ahmad