logo

HAUSA

Putin: Amurka ta taba tura masu leken asiri da dama a gwamnatin Rasha

2021-12-11 16:49:07 CRI

Putin: Amurka ta taba tura masu leken asiri da dama a gwamnatin Rasha_fororder_putin

A jiya Jumma’a, kafofin watsa labarai da dama na kasar Rasha sun gabatar da bayanai cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, ‘yan leken asiri na hukumar leken asiri ta kasar Amurka da yawan gaske sun taba aiki a cikin gwamnatin kasarsa, saboda Amurka tana son tsoma baki a harkokin cikin gidan Rasha.

Rahotanni sun nuna cewa, a ranar 9 ga wata, Putin ya halarci taron hukumar raya zamantakewar al’umma da hakkin bil adama na kasar Rasha, inda ya yi tsokaci cewa, a tsakiyar shekarun 1990, Amurkawa da yawan gaske sun taba yin aiki a hukumomin gwamnatin kasar Rasha a matsayin masu ba da shawara, daga baya an gano wadannan Amurkawan ‘yan leken asiri ne na hukumar CIA.

Putin ya jaddada cewa, al’amarin wani yunkuri ne na Amurka na neman tsoma baki a harkokin cikin gidan Rasha, kuma a wancan lokacin wasu masanan Amurka su ma sun taba yin aikin gine-ginen makaman nukiliya na Rasha, ya zuwa farkon karni na 21 kuwa, Rasha ta fitar da wadannan mutane, daga baya Rashar ta kara karfinta, musamman a fannin aikin soji.(Jamila)