logo

HAUSA

Mataimakin wakilin Sin a MDD: Tsarin demokuradiyyar tilas cin amanar ruhin demokuradiyya ne

2021-12-11 16:37:15 CRI

Jiya Jumma’a 10 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya jaddada yayin da ake binciken batun Sudan a taron kwamitin sulhun majalisar cewa, yanayin siyasar da kasar Sudan ke ciki yanzu ya shaida cewa, tsarin demokuradiyyar da kasashen ketare suka tilasta, tsoma baki ne suke yi, ta hanyar fakewa da demokuradiyya, ba demokuradiyya ce ta gaskiya ba.

Dai Bing ya ce, Sudan ta samu ci gaba a yunkurinta na shimfida zaman lafiya a kasar, kasar Sin ta yi maraba da wannan, lamarin da ya nuna cewa, muddin masu ruwa da tsaki na kasar suka mayar da moriyar kasa da al’ummar kasa a gaban kome, to za su daidaita matsalolin dake gabansu. A sa’i daya kuma, ya dace kasashen duniya su aiwatar da sulhu bisa adalci, kuma su martaba zabin al’ummar Sudan, bai kamata su tilastawa kasar amincewa da dabarunsu ba.

Kana ya yi nuni da cewa, ana iya tabbatar da tsarin demokuradiyya ne ta hanyoyi daban daban, ya dace kasashen duniya su tsara salon demomuradiyya bisa hakikanin yanayin da suke ciki.(Jamila)