logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a yi kokarin taimakawa Afirka wajen magance ta'addanci, da sauyin yanayi

2021-12-10 10:34:38 CRI

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a yi kokarin taimakawa Afirka wajen magance ta'addanci, da sauyin yanayi_fororder_211210-Yaya1-Zhang Jun

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a yi kokarin taimakawa kasashen Afirka, wajen magance ta'addanci da sauyin yanayi. Yana mai cewa, a 'yan shekarun baya-bayan nan, ta'addanci ya kawo babbar barazana ga nahiyar Afirka, musamman yankin Sahel.

Zhang Jun ya bayyana haka ne, yayin zaman muhawara da kwamitin sulhun MDD ya kira kan sha’anin tsaro, musamman ta’addanci da sauyin yanayi. Ya ce, yayin da ake fuskantar kalubaloli, kungiyar G5 Sahel wato kasashen Burkina Faso, da Chadi, da Mali, da Mauritania, da Jamhuriyar Nijar, sun hada kai don kara karfinsu na aiki, da zurfafa hadin gwiwar yaki da ta'addanci, matakin da ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron yankin. Kuma kasar Sin ta yaba da irin wannan kokarin.

Wakilin na kasar Sin ya ce, a cikin dogon lokaci, matakin soja kadai bai isa ya kawar da barazanar tsaro a yankin Sahel ba. A don haka, ya kamata a yi kokari don magance tushen rikice-rikice. A hannu guda kuma, ya kamata su ma kasashen duniya, su taimaka wa kasashen Afirka wajen magance matsaloli da dama, kamar tabarbarewar tattalin arziki, da karancin abinci da rikicin kabilanci, da kawar da ta'addanci, da ci gaba da tallafawa kasashen yankin wajen inganta karfin samar da tsaro, da ba da kariya ga al'ummomin dake yankunan karkara, da tabbatar da cewa, an kare kayayyakin da fararen hula ke amfani da su, kamar makarantu da asibitoci yayin rikice-rikice. (Ibrahim Yaya)