logo

HAUSA

Zhang: Jama'ar kasar Sin na more ingantaccen ’yancin dan Adam

2021-12-10 14:26:52 CRI

Zhang: Jama'ar kasar Sin na more ingantaccen ’yancin dan Adam_fororder_211210-yaya 3-better life

Wikilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, al'ummar kasar Sin na jin dadin kyakykyawan hakkin 'yancin dan Adam, da kuma ba da gudummawa mai kyau a fannin kare hakkin bil'adama a duniya. Zhang ya bayyana haka ne jiya Alhamis, a wani sako da ya aike albarkacin ranar kare hakkin dan-dama da ake bikin ta a kowace ranar 10 ga watan Disamba.

Ya ce, a karkashin jagorancin JKS, al’ummar Sinawa sun yi kokari sosai wajen yaki, da mutuntawa, da ma kare hakkin dan Adam, da sa kaimi ga yayata batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam baki daya.

Zhang ya ce, idan har ana son tabbatar da daidaito, to, akwai bukatar tabbatar da rarraba alluran rigakafi. Kana idan ana son a cimma daidaito, akwai bukatar kawar da wariyar launin fata bil hakki da gaskiya. Haka kuma, idan har ana son tabbatar da daidaito, akwai bukatar mutunta hakkin mutane a dukkan kasashe, na zabar hanyoyin ci gabansu da kansu.

Ya kara da cewa, hakkin dan Adam batu ne na duniya, amma hanyoyin da ake bi sun bambanta, kuma mafi kyau su ne wadanda suka dace da yanayin kowace kasa. A don haka, ya kamata kasashe su karfafa mu'amala da fahimtar juna, domin samun hanyar raya hakkin bil-adama da ta fi dacewa da yanayin kasa da bukatun jama'arta. Ya ce, an sha tabbatar cewa, demokuradiyya ko tsarin ’yancin dan adam da aka tilastawa wasu kasashe daga waje ba sa aiki. Don haka, muddin ana son a samu daidaito, akwai bukatar a nuna adawa da yadda ake siyasantar wadannan batutuwa da ma amfani da ma'auni biyu.  

Zhang ya ce, hakkin dan adam da demokuradiyya, ba dama ba ce da wasu tsirarun kasashe za su yi amfani da su, ko kuma wani makami da wata kasa za ta yi amfani da su wajen koda kanta, ko kafa wasu kananan kungiyoyi, ko tada sabon yakin cacar baka. Ya ce, abin takaici shi ne, wasu kasashen na amfani da ‘yancin dan Adam da demokuradiyya, a matsayin wata hujja wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, da haifar da rikici, da kuma sanyawa wasu kasashe takunkumi da gangan. Yana mai cewa, abin da suke yi, shi ne ya kawo babbar illa ga 'yancin dan Adam da tsarin demokradiyya. (Ibrahim Yaya)