logo

HAUSA

Ma'aikatar wajen Sin ta mayar da martani ga kalaman Amurka a "taron dimokuradiyya"

2021-12-10 16:39:58 CRI

Ma'aikatar wajen Sin ta mayar da martani ga kalaman Amurka a "taron dimokuradiyya"_fororder_汪文斌

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin, ya jagoranci taron manema labaran da aka saba gudanarwa Jumma’ar nan. Yayin taron, wani dan jarida ya yi tambaya cewa, a ranar farko ta “taron kolin dimokuradiyya”, da Amurka ta kira, shugaban Amurka Biden ya bayyana cewa, a cikin shekaru goma da suka wuce, mulkin danniya da kama-karya sun yi yunkurin fadada tasirinsu kan kasashen dake bin tsarin dimokuradiyya, ko mene ne martanin kasar Sin kan hakan?

Wang Wenbin ya ce dimokuradiyya kimar bai daya ce ta dukkan bil adama, ba wani makami ba ne na ciyar da tsarin kasa gaba ba. Domin kiyaye matsayin mulkin mallaka, Amurka tana fakewa da tutar dimokuradiyya, tana haifar da rarrabuwar kawuna da adawa, tare da lalata tsarin kasa da kasa karkashin jagoranin MDD da tsarin kasa da kasa wanda ya dogara da dokokin kasa da kasa. Wannan adawa ne da tsarin demokradiyya karara.(Ibrahim)