logo

HAUSA

Wang Wenbin: Walwalar jama’a ne ma’aunin nasarar kare hakkin dan adam

2021-12-10 20:34:23 CRI

Yau Juma’a 10 ga watan Disamba ne ranar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa. Kuma sakamakon furucin da wasu kasashen yammacin duniya ke ta yi, game da halin da kasar Sin ke ciki a wannan fanni, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce walwalar jama’a ne ma’aunin nasarar kare hakkin dan adam a ko ina.

Wang wanda ya bayyana hakan a yau Juma’a, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce ana iya gane nasarar kare hakkin bil adama ne kawai idan al’umma suna samun moriya, suna cikin farin ciki da tsaro. Domin kuwa rayuwa mai cike da farin ciki, ita ce babbar nasarar kare hakkin bil adama. (Saminu)