logo

HAUSA

Afrika CDC: Kasashen Afrika 11 sun samu rahoton bullar nau’in Omicron na cutar COVID-19

2021-12-10 10:33:33 CRI

Afrika CDC: Kasashen Afrika 11 sun samu rahoton bullar nau’in Omicron na cutar COVID-19_fororder_211210-Ahmad 1-Afrika CDC

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar cewa wasu kasashen Afrika 11 sun samu rahoton bullar nau’in cutar COVID-19 ta Omicron.

John Nkengasong, daraktan cibiyar Africa CDC, ya bayyanawa manema labarai cewa an samu karin kasashen Afrika bakwai da aka samu rahoton bullar nau’in Omicron a makon da ya gabata, inda kawo yanzu adadin kasashen ya kai 11.

A cewar Afrika CDC, kasashen sun hada da Afrika ta kudu, Botswana, Najeriya, Ghana, Uganda, Zambia, Senegal, Tunisia, Mozambique, Namibia, da Zimbabwe.

A ranar Laraba, kungiyar tarayyar Afrika AU ta yi gargadin cewa dokar hana tafiye-tafiyen da wasu kasashe suka sanya sakamakon bullar sabon nau’in Omicron na cutar COVID-19 ya haifar da karancin hada hadar kasuwanci da zirga-zirgar jama’a, lamarin da ke haifar da mummunan tasiri ga kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)