logo

HAUSA

Nicaragua ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan

2021-12-10 11:10:27 CRI

Nicaragua ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan_fororder_211210-Ahmad 3-Nicaragua

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Nicaragua ta sanar a jiya Alhamis cewa, kasar Nicaragua ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan.

Cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ta fitar a Managua ta ce, “Gwamnatin jamhuriyar Nicaragua ta ayyana cewa ta amince da manufar kasar Sin daya tak a duniya."

A cewar sanarwar, “Jamhuriyar jama’ar kasar Sin ita ne kadai halastacciyar gwamnati wadda ke wakiltar dukkan kasar Sin, kuma Taiwan wani bangare ne na babban yankin kasar Sin wadda ba za a taba raba su ba."

Sanarwar tace, “A yau gwamnatin jamhuriyar Nicaragua ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan kuma ta dakatar da dukkan wata hulda da mu’amala a hukumance da yankin Taiwan." (Ahmad Fagam)