logo

HAUSA

Shugaban WHO: Nau’in Omicron na iya canza yanayin yaki da cutar COVID-19

2021-12-09 13:50:16 CRI

Shugaban WHO: Nau’in Omicron na iya canza yanayin yaki da cutar COVID-19_fororder_211209-Omicron

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, wasu daga cikin siffifon nau'in Omicron, ciki har da yaduwarsa a duniya, da kuma yadda yake yawan sauyawa, sun nuna cewa, nau’in zai iya yin babban tasiri kan yanayin cutar ta COVID-19.

Tedros ya bayyana haka ne jiya Laraba, yayin wani taron manema labarai, inda ya yi gargadin cewa, nau’in na Omicron zai iya kara yaduwa fiye da ragowar nau’in cutar ta COVID-19, ganin yadda ya zuwa yanzu ya yadu zuwa kasashe 57.

A cewar babbar masaniyar kimiya a hukumar WHO Soumya Swaminathan, har yanzu lokaci bai yi ba, da za a ce nau’in na Omicron zai iya rage tasirin rigakafin cutar. (Ibrahim Yaya)