logo

HAUSA

Ma Zhaoxu: Sin na da fatan aiki tare da MDD wajen ingiza shirin bunkasa ci gaban duniya

2021-12-09 20:31:51 CRI

Ma Zhaoxu: Sin na da fatan aiki tare da MDD wajen ingiza shirin bunkasa ci gaban duniya_fororder_Ma Zhaoxu

A yau Alhamis ne aka gudanar da taron karawa juna sani, mai taken "Bunkasa shirin raya ci gaban duniya, da hadin gwiwar aiwatar da ajandar samar da ci gaba mai dorewa zuwa shekarar 2030".

Yayin taron, wanda aka kira a nan birnin Beijing, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, ya jaddada cewa, Sin na da shirin yin aiki tukuru tare da MDD, wajen ingiza shirin bunkasa ci gaban duniya.

Ma Zhaoxu ya kara da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da shirin bunkasa ci gaban duniya, ya kuma yi kira da sassan kasa da kasa da su sa kaimi wajen ingiza kawance, da yayata kudirorin ci gaba marasa gurbata muhallin duniya. Ya ce wannan ce shawarar kasar Sin game da tallafawa kasashe masu tasowa da dabarun ci gaba.

Tun bayan kaddamar da shirin raya ci gaban duniya sama da watanni 2 da suka gabata, shirin ke kara samun karbuwa daga sassan kasa da kasa daban daban. (Saminu)