logo

HAUSA

Shugaban kungiyar FIVB: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022 za ta taimaka wajen kawar da mummunar fassarar kasar Sin

2021-12-09 10:15:31 CRI

Shugaban kungiyar FIVB: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022 za ta taimaka wajen kawar da mummunar fassarar kasar Sin_fororder_211209-Olympics

Shugaba mai girmamawa na kungiyar wasan kwallon raga ta duniya (FIVB) Wei Jizhong ya bayyana cewa, ko jami'an gwamnatocin wasu kasashen yammacin duniya sun halarci gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022 da birnin Beijing zai karbi bakunci ko a’a, da kyar hakan ya yi wani tasiri a gasar . 

Wei Jizhong ya bayyana haka ne a jiya Laraba, yayin da yake mayar da martani ga sanarwar da Amurka ta fitar na baya-bayan nan cewa, ba za ta tura jami'anta zuwa gasar Olympics din ba

Wei ya ce Amurka ta yi hakan ne, da niyyar kawo cikas da kuma lalata wasannin na 2022, amma burinsu ba zai cika ba.

Wei ya yi nuni da cewa, a cikin 'yan shekarun nan, wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na yammacin duniya, sun nemi bata sunan kasar Sin, lamarin da ya rikitar da al'ummar kasashen waje da dama. Tun bayan barkewar cutar COVID-19, ake samun karuwar rashin fahimta game da kasar Sin a wasu kasashen yammacin duniya, yayin da aka rage ko ma dakatar da mu'amala tsakanin kasa da kasa.

Amma a cewar Wei, kamar yadda gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta 2008 ta yi, wasannin lokacin sanyi na 2022 ma, za su ba da wata dama ga jama'ar yammacin duniya, su fahimci hakikanin kasar Sin. (Ibrahim)