logo

HAUSA

Afghanistan ta karbi karin gudunmawar riga-kafin Sinopharm na kasar Sin

2021-12-09 10:45:41 CRI

Afghanistan ta karbi karin gudunmawar riga-kafin Sinopharm na kasar Sin_fororder_211209-Afghanistan

Ranar Laraba gudunmawar alluran riga-kafin COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta samar ya isa Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

An gudanar da bikin mika riga-kafin a filin jirgin saman kasa da kasa na Kabul, wanda ya samu halartar jakadan kasar Sin a Afghanistan Wang Yu, da mataimakin ministan lafiyar kasar Afghanistan Abdul Bari Omar.

Da yake jawabi a wajen bikin, Wang ya bayyana cewa, tun bayan sauyawar yanayin siyasar kasar Afghanistan, kasar Sin ta sanar da ba da gudunmawar alluran riga-kafin miliyan uku da sauran kayayyakin kiwon lafiya ga kasar Afghanistan.

A nasa bangaren, Omar ya bayyana farin cikinsa ga gwamnatin kasar Sin bisa samar da gudunmawar da kuma taimakon ta take baiwa kasar Afghanistan. Ya ce gudunmawar tana da matukar muhimmanci ga al’ummar kasar Afghanistan musamman a wannan mawuyacin halin da kasar ke ciki.

Wannan shi ne rukuni na biyu na riga-kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm wanda kasar Sin ta baiwa Afghanistan. A wata Yunin bana da ya gabata, kasar Sin ta aike da gudunmawar riga-kafin COVID-19 ga kasar Afghanistan. (Ahmad Fagam)