logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Sin ya yi watsi da rahoto maras tushe da BBC ta yada game da Xinjiang

2021-12-09 15:27:01 CRI

Ofishin jakadancin Sin ya yi watsi da rahoto maras tushe da BBC ta yada game da Xinjiang_fororder_BBC

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Birtaniya ya yi watsi da rahoto maras tushe da BBC ta yada dake shafar batun yankin Xinjiang na kasar Sin, yana mai cewa, babu wani batu da ake kira wai “aikin tilas” a yankin, kuma bayanan zargin na wanda aka tattauna da shi ya kasance karya ce tsagwaronta.

Yayin da yake bayani ga kafar watsa labaran BBC, mutumin da aka tattauna da shi ya yi ikirarin an saka shi yin “aikin tilas” a Xinjiang, kakakin ofishin jakadancin ya ce karya ce, kuma ko da an maimaita kalaman nasa sama da sau dubu, har yanzu yana nan a matsayin karya.(Ahmad)