logo

HAUSA

Dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa na BDS zai fadada hadin gwiwar samun nasara tare

2021-12-09 15:18:54 CRI

Dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa na BDS zai fadada hadin gwiwar samun nasara tare_fororder_beidou

Kasar Sin da kasashen Larabawa, za su fadada hadin gwiwarsu ta hanyar samun nasara tare wajen amfani da tsarin tauraron dan adam na BeiDou da kasar Sin ta kirkira, kamar yadda dandalin hadin gwiwar Sin da Larabawa na BDS karo na uku ya nuna.

A bisa tsarin hadin gwiwar da aka sanyawa hannu a yayin dandalin tattaunawar, kasar Sin da kasashen Larabawa, za su yi hadin gwiwa tare da aiwatar da ayyukan gwaji a muhimman fannoni na dandalin BDS da tsarin zirga-zirga na tauraron dan adam na duniya (GNSS) a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023.(Ibrahim)