logo

HAUSA

Sin da Rwanda sun sanya hannu kan yarjejeniyar soke biyan haraji ninki biyu

2021-12-09 10:28:27 CRI

Sin da Rwanda sun sanya hannu kan yarjejeniyar soke biyan haraji ninki biyu_fororder_211209-Ruwanda

Kasashen Sin da Rwanda sun sanya hannu kan yarjejeniyar soke biyan kudaden haraji ninki biyu bisa la’akari da yanayin biyan harajin kudaden shiga da kuma kiyaye dukkan matakan dake shafar tsarin biyan harajin.

Yarjejeniyar wacce aka sanyawa hannu a ranar Talata, inda jakadan kasar Sin a Rwanda Rao Hongwei, da ministan kudi da tsara tattalin arzikin kasar Rwanda Uzziel Ndagijimana suka jagoranta.

Jakadan ya ce, shekaru sama da 50 da suka gabata tun bayan kafa huldar diflomsiyyarsu, dangakatar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da fadada a fannonin tattalin arziki da kasuwanci, inda kasar Sin ta kasance a matsayin kasa mafi girma dake gudanar da ayyukan kwangiloli a kasar Rwanda, kana daya daga cikin manyan abokan huldar cinikayyar kasar.

Ndagijimana ya ce, sanya hannu kan yarjejeniyar zai kara daga matsayin kasar Rwanda a matsayin wani muhimmin wurin da kamfanonin kasar Sin suke son zuba jari.

Ministan ya ce, za a ci gaba da samun karin jari mai yawan gaske daga kasar Sin a kasar Rwanda, kuma a shirye kasar take ta hada gwiwa da kuma yin aiki tare da kasar Sin wajen zurfafa hakikanin hadin gwiwarsu a fannonin dake shafar kyautata tsarin biyan kudaden haraji da kuma bunkasa kyakkyawar huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Ahmad Yaya)