logo

HAUSA

An Zartas Da Takardar Burin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Zuwa Shekarar 2035

2021-12-08 21:59:04 CMG

An Zartas Da Takardar Burin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Zuwa Shekarar 2035_fororder_taro

Daga ranar 29 zuwa ta 30 ga watan Nuwamban da ya gabata, an gudanar da taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC, a Dakar, hedkwatar kasar Senegal, inda mahalarta taron suka zartas da takardar burin hadin gwiwar Sin da Afirka zuwa shekarar 2035.

Ban da wannan kuma, a jiya Talata, hukumar raya kauyuka ta kasar Sin, da cibiyar rage talauci a duniya ta kasar Sin, sun kira wani taron tattauna batun rage talauci da neman samun ci gaba, karkashin laimar dandalin FOCAC, inda aka sanya wa taron taken “Hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin rage talauci: manufofin raya kauyuka da yadda ake gudanar da su”. (Bello Wang)

Bello