logo

HAUSA

Gobara ta halaka fursunoni 38 a gidan yari a tsakiyar kasar Burundi

2021-12-08 13:55:38 CRI

Gobara ta halaka fursunoni 38 a gidan yari a tsakiyar kasar Burundi_fororder_i02-38 inmates died in prison fire in central Burundi

Mataimakin shugaban kasar Burundi, Prosper Bazombanza ya bayyana bayan ya ziyarci gidan yarin Gitega da ke tsakiyar kasarsa, a wani taron manema labarai da aka shirya a birnin Bujumbura, babban birnin kasar cewa, a kalla fursunoni 38 ne suka mutu, yayin da wasu 69 suka jikkata, sakamakon wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar ranar Talata a gidan yarin.

Prosper Bazombanza yana mai cewa, gobarar ta tashi, biyo bayan wasu na’urori da wayoyin lantarki da fursunoni suka hada ba kamar yadda ya kamata ba a cikin gidan yarin.

Ya kuma yi amfani da wannan dama, wajen gargadin ’yan kasar ta Burundi da ke zaune a cikin al'ummomi kamar makarantu, da barikokin soja ko 'yan sanda, da su guji hada irin wadannan layukan wuta dake iya haddasa hadari. A don haka, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta biya kudin asibiti ga wadanda suka jikkata.

Bazombanza ya bukaci ma'aikatar hadin kai, da ta samar da kayayyakin abinci, da matsuguni kamar tantuna da katifu ga gidan yarin kasar, don baiwa fursunonin damar zama cikin yanayi mai kyau.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatar samar da ababen more rayuwa, da ta gano abubuwan da ake bukata na gyara gidan yarin, wanda a halin yanzu yana dauke da fursunoni sama da 1,500, maimakon farsunoni 400 kawai da ya kama ya dauka. (Ibrahim Yaya)