logo

HAUSA

’Yan saman jannati na kumbon Shenzhou-12 sun gana da al’umma

2021-12-08 11:27:48 CRI

’Yan saman jannati na kumbon Shenzhou-12 sun gana da al’umma_fororder_a8ec8a13632762d0467ca7b31b2d82f3503dc643

A jiya Talata, cibiyar horar da ’yan saman jannati na kasar Sin ta shirya taron ganawa a tsakanin ’yan saman jannati na kumbon Shenzhou-12 da ya dawo doron duniyarmu da manema labarai. A yayin taron, an ga ’yan saman jannatin uku cikin karin koshin lafiya kamar yadda ake fata.

A matsayinsa na dan saman jannati na kasar Sin na farko da ya shafe sama da kwanaki 100 a cikin sararin samaniya, malam Nie Haisheng ya je sararin samaniya har sau uku, ya ce, a yayin da harkokin sararin samaniya ke dada bunkasa, za a samu karin nasarori ta fannin nazarin sararin samaniya. Yana mai cewa,“Bisa saurin bunkasuwar fasahohin zirga-zirgar sararin samaniya, Sinawa za su samu karin ci gaba ta fannin nazarin sararin samaniya. Bayan da kasar Sin ta kammala gina tashar binciken sararin samaniya na kanta, a ganina za a samu jama’a daga ciki da wajen kasar Sin da za su ziyarci tashar, ciki har da wadanda ba su da nasaba da sana’ar da ta shafi sararin samaniya, zamanin da ba shi da nisa. Sai dai dole ne a shirya, sabo da tabbas akwai sharudan da aka gindaya wajen zuwa sararin samaniya, musamman ta fannonin koshin lafiya da tunani, kuma mun san cewa wadanda suka shirya ne, za su ci gajiwar wannan dama. "(Lubabatu)