logo

HAUSA

Kakakin Beijing 2022: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing tana nuna ruhin hadin kai

2021-12-08 13:54:33 CRI

Kakakin Beijing 2022: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing tana nuna ruhin hadin kai_fororder_i03-Beijing Winter Olympics shows spirit of solidarity

Mai magana da yawun kwamitin shirya gasar wasannin Olympics da birnin Beijing zai karbi bakunci a shekarar 2022, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata hira ta musamman da aka yi da shi cewa, a bisa la’akari da taken gasar Olympics wato "Sauri, karfi da kasancewa tare," rashin sanya siyasa da nuna goyon baya ga wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing 2022, shi ne babban ra'ayi na kasa da kasa.

Kakakin ya ce siyasantar da wasanni, ya saba wa tsarin yarjejeniya ta Olympics. Domin yin haka, yana cutar da muradun bai daya na 'yan wasa da kuma babban Iyalin Olympics.

An dai amince da kudurin sulhu na gasar Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing bisa yarjejeniya tare da hadin gwiwar mambobi kasashe 173 a taron MDD karo na 76. Shugaban IOC Thomas Bach ya sha bayyana nasarar gudanar da gasar ta Beijing ta shekarar 2022, kuma da yawa daga cikin shugabannin kungiyoyin kasa da kasa (IFs) ma, sun nuna goyon baya.

Dangane da sanarwar da Amurka ta yi na kaurace wa wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 da birnin Beijing zai karbi bakunci, kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC) ya nanata cewa, wasannin Olympics da 'yan wasa sun fi karfin batu na siyasa. A cewar kakakin, yanzu haka dai, an kammala dukkan shirye-shiryen wasannin da birnin Beijing zai karbi bakunci. (Ibrahim Yaya)