logo

HAUSA

An wallafa littafin jawaban Xi kan kare hakkin dan Adam

2021-12-08 13:53:11 CRI

An wallafa littafin jawaban Xi kan kare hakkin dan Adam_fororder_i05-Book of Xi

Kamfanin dab’i na kwamitin koli na JKS, ya buga littafin jawaban shugaban kasar Sin Xi Jinping da aka zabo, kan yadda ake mutuntawa da kare hakkin dan Adam a fadin kasar tare da raba su a sassan kasar.

Littafin mai kunshe da jigogi guda tara, ya kunshi jawabai 335 da aka tsamo daga rahotanni sama da 160, da jawabai, da wasiku na taya murna da umarnin da Xi, kana babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban kwamitin tsakiya na soja ya bayar. (Ibrahim)