logo

HAUSA

Xi ya mika wasikar taya murnar bude dandalin tattaunawa hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa na 2021

2021-12-08 20:33:26 CRI

Xi ya mika wasikar taya murnar bude dandalin tattaunawa hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa na 2021_fororder_1000

Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika wasikar taya murnar bude taron dandalin tattaunawa batun hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa na shekarar 2021.

Cikin wasikar ta sa, Xi ya ce, hakkin dan Adam na nuni ga ci gaban bil Adam, yana kare mutuncin bil Adam, da kare ikon bil Adam, kuma shi ne burin al’ummomin kasa da kasa.

A yau Laraba, aka bude taron dandalin tattaunawa hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa na shekarar 2021 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Kuma taken taron shi ne “Ikon al’umma da kare hakkin bil Adam na kasa da kasa”. (Maryam)