logo

HAUSA

Thomas Bach ya jinjinawa nasarar da tashar CMG mai yada ruhin gasar Olympic ta cimma

2021-12-08 19:27:59 CRI

Thomas Bach ya jinjinawa nasarar da tashar CMG mai yada ruhin gasar Olympic ta cimma_fororder_bach

Shugaban kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa da kasa IOC, Mr. Thomas Bach, ya gabatarwa babban daraktan rukunin gidajen radiyo da talabijin na Sin ko CMG Mr. Shen Haixiong wata wasika, wadda a cikin ta ya jinjinawa nasarar da tashar CMG mai yada ruhin gasar Olympic ta cimma, yana mai cewa, kafar talabijin ta CCTV ta ciri tuta, a kokarin ta na yayata ruhin gasar Olympic.

Mr. Bach ya kara da cewa, “Ina matukar farin ciki da jin cewa, tashar CMG ta watsa gasar Olympic, ta samu karbuwa sosai tsakanin Sinawa, ta kuma cimma nasarori a dukkanin ayyukan da take gudanarwa. Ina matukar godiya ga wannan tasha bisa kwazon ta".

An kafa tashar CMG ta watsa gasar Olympics ne gabanin gasar Olympic ta lokacin hunturu da birnin Beijing zai karbi bakunci a badi, ta kuma ba da gudummawa wajen yayatawa, da kuma bunkasa ruhin gasar Olympic din dake tafe.  (Saminu)