logo

HAUSA

Kasashen Sin da Somaliya sun kulla yarjejeniyar sabunta cibiyoyin watsa labarai

2021-12-07 14:02:33 CRI

Kasashen Sin da Somaliya sun kulla yarjejeniyar sabunta cibiyoyin watsa labarai_fororder_211207-yaya 4

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Somaliya jiya Litinin, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da ma'aikatar yada labaran kasar, domin zamanintar da cibiyoyin yada labarai na kasar.

Yarjejeniyar fahimtar juna wadda jakadan kasar Sin dake Somaliya Fei Shengchao da ministan yada labarai na Somaliya, Osman Dubbe suka sanya wa hannu, ta zayyana wasu ayyuka da suka shafi gyarawa da samar da kayan aikin rediyon Mogadishu, da gidan wasan kwaikwayo na kasa da kuma kamfanin dillancin labarai na kasar Somaliya (SONNA).

Dubbe ya ce, yarjejeniyar na da matukar muhimmanci ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma ta share fagen kara yin hadin gwiwa a nan gaba. (Ibrahim Yaya)