logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gudanar da taro na 6 na "1+6" da shugabannin manyan kungiyoyin tattalin arziki na duniya

2021-12-07 11:37:24 CRI

Firaministan kasar Sin ya gudanar da taro na 6 na "1+6" da shugabannin manyan kungiyoyin tattalin arziki na duniya_fororder_1128137657_16388151101611n

Jiya da dare ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gudanar da taro na 6 na "1+6" tare da shugabannin manyan kungiyoyin tattalin arziki na kasa da kasa, ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugaban babban bankin duniya David Malpass, da babbar darektar asusun ba da lamuni ta duniya na IMF Kristalina Georgieva, da Ngozi Okonjo-Iweala, babbar darektar kungiyar cinikayya ta duniya ta WTO, da Guy Ryder, darekta-janar na kungiyar kwadago ta duniya, da Mathias Cormann, babban sakataren kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasa, da Klaas Knot, shugaban hukumar kula da harkokin kudi, sun halarci taron. Inda suka tattauna tare da yin mu’amala kan yadda za a sa kaimi ga samun farfadowar tattalin arzikin duniya, da karuwar tattalin arziki mai dorewa bayan annobar COVID-19, gami da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata

Firaminista Li Keqiang ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana hade da tattalin arzikin duniya sosai, kuma Sin za ta kara bude kofarta ga ketare nan gaba, ta yadda kasashen duniya za su ci gajiyar ci gaban kasar wajen raya kansu. Li ya kara da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban a karkashin jagorancin kungiyar WTO, da ma sa kaimi ga ’yancin cinikayya da zuba jari.

A nata jawabin, Madam Ngozi Okonjo-Iweala, babbar darektar kungiyar cinikayya ta duniya ta jinjinawa manyan nasarorin da Sin ta samu cikin shekaru 20 da suka gabata tun bayan da ta shiga kungiyar. Ta ce,

“Kasar Sin abokiyar kasashe masu tasowa ne, inda ta nuna yadda za a iya samun ci gaba da ma yaki da talauci ta hanyar raya harkokin cinikayya. Muna sa ran Sin za ta kasance a kan gaba wajen goyon bayan yadda za a yiwa WTO gyaran fuska.”