logo

HAUSA

Yankin gonaki mafi girma na kasar Sin ya samu yabanya mai yalwa

2021-12-07 19:40:47 CRI

Yankin gonaki mafi girma na kasar Sin ya samu yabanya mai yalwa_fororder_丰收

Manoma a yankin arewa maso gabashin kasar Sin, da ake yiwa lakabi da rumbun kasar, wanda ya kunshi lardunan Heilongjiang, da Liaoning da Jilin, sun samu yabanyar hatsi mai yalwa a kakar bana.

Alkaluman kididdiga daga hukumar kididdigar kasar NBS ta fitar a jiya Litinin, sun nuna yadda a bana, jimillar hatsin da lardunan suka girbe ya kai tan miliyan 144.5, adadin da ya karu da kaso sama da tan miliyan 7.6 a shekara guda.  (Saminu)