logo

HAUSA

Birtaniya ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ta hana al’ummun ta shiga kasar

2021-12-07 20:04:57 CRI

A ranar Lahadin karshen makon jiya ne, jaridar Guardian da ake wallafawa a Najeriya, ta rawaito babban ministan lafiya da walwalar jama’a na Birtaniya na cewa, a baya bayan nan, an samu wasu mutane dauke da nau’in Omicron na cutar COVID-19 a kasar, kuma mutanen na da alaka da matafiya daga Najeriya.

Ministan ya kara da cewa, sakamakon hakan ne ya sa gwamnatin Birtaniya, ta sanya Najeriya tare da wasu karin kasashen 10, cikin jerin kasashe da ta dakatar da al’ummun su shiga kasar, tun daga jiya Litinin 6 ga wata.

Hakan na nufin dukkanin matafiya da suka kasance a Najeriya tsawon kwanaki 10 da suka gabata, ba za su samu izinin shiga Birtaniya ba.  (Saminu)