logo

HAUSA

Afirka na shirin kara karfin samar da allurar rigakafi da kanta

2021-12-07 16:45:05 CRI

Afirka na shirin kara karfin samar da allurar rigakafi da kanta_fororder_211207-yaya 5-African Vaccine

Jiya ne cibiyar kandagrki da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta gudanar da wani babban taro na hadin gwiwar samar da allurar rigakafin cutar a Kigali, babban birnin kasar Rwanda. Mahalarta taron sun yi imanin cewa, saboda rashin adalci game da rarraba allurar rigakafi da wasu dalilai, ya zama wajibi a kara karfin samar da rigakafin a Afirka.

Manufar taron na kwanaki biyu, ita ce kara tattaunawa kan ci gaban samar da rigakafin. Babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a taron cewa, sama da kashi 18 cikin 100 na sabbin alluran rigakafin COVID-19 suna zuwa kasashen G20 ne, yayin da kasashe masu karamin karfi ke samun kashi 0.6 cikin 100 na allurar rigakafi a duniya. Rashin adalci dangane da rabon alluran rigakafin na COVID-19, musamman bullar nau’in cutar na Omicron, ya nuna muhimmancin inganta karfin samar da allurar rigakafi a Afirka. (Ibrahim Yaya)