<![CDATA[Omicron: Shugaban WHO ya soki kasashen da ke hana matafiya daga Afirka shiga kasashensu]]>Babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom ya yi Allah wadai da kasashen da suka sanya dokar hana zirga-zirga a kan matafiya daga kudancin Afirka, saboda bullar sabon nau’in Omicron na COVID-19.

Masana kimiyyar Afirka ta Kudu ne suka fara gano nau'in cutar, wanda tun daga lokacin aka kara gano shi a wasu kasashe da dama na duniya.

Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa, nau’in COVID-19 na Omicron ya bulla a Turai tun kafin a sanar da hana tafiye-tafiye.

Ya kara da cewa, mutuntawa yana da nasaba da kwarewar kimiyya da fasaha a kasashen Afirka da kuma nuna gaskiya da musayar ra'ayi, gami da bayanan da suka shafi bambancin damuwa game da nau’in na Omicron. Yana mai cewa, wannan yana taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya ga dukkan mutane a ko'ina.

Shugabannin Afirka dai, sun yi Allah wadai da dokar hana zirga-zirgar. A maimakon haka, sun yi kira ga kasashe masu hannu da shuni, da su yaba kokarin nahiyar wanda ya ba da damar gano nau'in cutar a kan lokaci.

Kasashen da suka takaita tafiye-tafiye sun hada da Amurka, wacce ta haramtawa matafiya daga kaashen Afirka ta kudu, da Botswana, da Zimbabwe, da Namibia, da Lesotho, da Eswatini, da Mozambique da Malawi shiga cikin kasarta. (Ibrahim)

]]>