logo

HAUSA

Sin za ta kara inganta zaman rayuwar al’ummar karkara

2021-12-06 10:43:11 CRI

Sin za ta kara inganta zaman rayuwar al’ummar karkara_fororder_211206-China-Ahmad.docx

Kasar Sin ta fidda shirin raya kasa na shekaru biyar game da inganta yanayin zaman rayuwar karkara a kokarinta na daga matsayin kyautata yanayin zaman rayuwar al’umma mazauna karkara.

Manufar bunkasa yanayin zaman rayuwar mazauna karkara yana da alaka da kyautata rayuwar manoma da gina kayatacciyar kasar Sin, kamar yadda sanarwar hadin gwiwa ta shirin wanda babban ofishin kwamitin tsakiyar JKS da babban ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin suka fidda.

Nasarorin da aka cimma a yankunan karkara tun bayan da kasar Sin ta kaddamar da shirin kyautata yanayin zaman rayuwar mazauna karkara na shekaru uku a shekarar 2018, shirin ya bukaci a kara kokarin gaggauta inganta yanayin zaman rayuwar yankunan karkara.

Nan da shekarar 2025, ana fatan yanayin muhallin karkara zai samu matukar kyautatuwa, yayin da ake kokarin daga matsayin aiki samar da ban dakuna a yankunan karkara, da kuma tsaftace dattin ban dakuna yadda ya kamata.

Shirin ya kuma bukaci kokarin kara cigaba da kulawa ga sarrafa yawan shara a yankunan karkara tare da kara bada kariya ga magidantan yankunan karkara ba tare da sun gamu da illoli daga ayyukan sarrafa sharar ba nan da shekarar 2025. (Ahmad)