logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da shirin shekaru 5 na bunkasa bangaren masana'antu ba tare da gurbata muhalli ba

2021-12-06 11:48:49 CRI

Kasar Sin ta fitar da shirin shekaru 5 na bunkasa bangaren masana'antu ba tare da gurbata muhalli ba_fororder_211206-green developmen-Yaya

Kwanakin baya ne, kasar Sin ta fitar da wani shiri na raya sassan masana'antu maras gurbata muhalli, a cikin shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 wanda za a aiwatar daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, abin da ke zama ci gaba a kokarin kasar na samun bunkasuwar karancin sinadarin Carbon.

A bisa shirin, za a kara habaka samar da makamashi da albarkatun kasa, yayin da ci gaban sassan masana’antu ba tare da gurbata muhalli ba zai kara habaka nan da shekarar 2025, tare da aza harsashi mai karfi na kololuwar fitar da hayakin Carbon a sassan masana'antu nan da shekarar 2030. Za kuma a rage yawan fitar da hayaki mai gurbata muhalli a muhimman sassa da kashi 10 cikin 100.

Bugu da kari, za a kafa tsarin masana'antun sakar da kayayyaki maras gurbata muhalli a muhimman sassa da yankunan kasar nan da shekarar 2025, inda darajar kasuwar masana'antun maras gurbata muhalli ya kai yuan tiriliyan 11, kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.73. (Ibrahim Yaya)