logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen Sin ta fidda rahoto kan matsayin demokaradiyya a Amurka

2021-12-05 16:31:03 CRI

Ma’aikatar wajen Sin ta fidda rahoto kan matsayin demokaradiyya a Amurka_fororder_amurka

Shafin intanet na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, a yau Lahadi ya fidda rahoto mai taken “Matsayin demokaradiyya a Amurka."

Bisa dogaro da hujjoji da kuma ra’ayoyin masana, rahoton yana son bankado gazawa da yin karan zaye ga demokaradiyya a kasar Amurka da kuma hadarin dake tattare da yada irin wannan demokaradiyyar zuwa ga sauran kasashen duniya. Ana fatan Amurka za ta inganta tsarinta, da irin salon da take amfani da shi a demokardiyya, kana ta sauya hanyar mu’amalarta da sauran kasashen duniya, in ji rahoton.

Rahoton ya ce, ita dai demokaradiyya batu ne na muradun bai daya na dukkan bil adama. Hakki ne na dukkan kasashen duniya, ba wai ya kebanta ga wasu ‘yan tsiraru ba ne, rahoton ya kara da cewa, demokadiyya tana iya daukar salo iri daban daban, kuma babu wani batu na cewa tsarin wani bangare shi ne ya fi dacewa sama da na kowa.

Ya ci gaba da cewa, sam ba tsarin demokaradiyya ba ne a auna salon demokaradiyyar sauran kasashen duniya da wani tsari guda daya tilo, ko kuma kwatanta tsarin siyasar kasashe daban daban da wani tsari daya tak ko mahangar wani bangare daya.

Rahoton ya yi cikakken bayani game da halayyar nuna wariya, da illolin dake tattare da tsarin siyasar kasar Amurka daga bangarori uku: na farko, tsarin na kumshe da tarin matsaloli masu yawan gaske, na biyu akwai kura-kurai da rudani a tsarin demokaradiyyar kasar, sannan na uku akwai haddura masu tarin yawa dake tattare da rungumar salon demokaradiyyar Amurka ga sauran kasashen duniya.

A cewar rahoton, abin da ya fi dacewa ga Amurka a halin yanzu shi ne, ta tsaya tsayin daka wajen yin aiki tukuru domin tabbatar da ganin ta biya muradun hakkokin demokaradiyya na al’ummarta, kana ta inganta tsarin demokaradiyyarta maimakon dora muhimmanci kan neman maye gurbin tsarin demokaradiyyar sauran kasashe da salo irin nata.

Abin da ya fi dacewa ga Amurka shi ne, ta yi kokarin sauke karin nauyin kasa da kasa dake wuyanta, kuma ta samar da karin alkahirai ga al’ummar duniya maimakon kokarin kakabawa sauran kasashen duniya tsarin demokaradiyyar da take amfani da shi, da yin amfani da damammakinta wajen kawo baraka a tsakanin kasa da kasa, ko kuma ta hanyar fakewa da kai dauki, tana kokarin yin mamaya, da kai hare hare kan sauran kasashen duniya da sunan neman kafa tsarin demokaradiyya.(Ahmad)