logo

HAUSA

Xi ya yi alkawarin tabbacin goyon bayan huldar bangarori daban daban

2021-12-05 20:46:04 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, aniyar kasar Sin ta goyon bayan huldar bangarori daban daban ba za ta taba sauyawa ba, Xi ya bayyana hakan ne a yau Lahadi cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a wajen bude dandalin taron tattaunawar kasa da kasa na shekarar 2021 a cibiyar taron kasa da kasa ta Congdu dake birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

Xi ya yi kiran a kiyaye huldar kasa da kasa karkashin tsarin MDD, da mutunta dokokin kasa da kasa wadanda ke kumshe a kundin dokokin kasa da kasa, da kuma bin muhimman tsarukan huldar kasa da kasa bisa dacewa da yarjejeniyar MDD, da daga matsayin muradun bai daya na bil adama dake shafar zaman lafiya, ci gaba, tabbatar da daidaito, adalci, demokaradiyya da kuma ‘yanci.

Game da batun shugabancin duniya kuwa, shugaba Xi ya ce, yana da matukar muhimmanci a ci gaba da kiyaye dukkan matakan da za su daga matsayin alkiblar tsarin demakaradiyya a bisa tashen huldar kasa da kasa, a kara yawan wakilci da amon muryar kasashe masu tasowa a harkokin kasa da kasa, kana a tafiyar da tsarin shugabancin duniya bisa adalci da samar da daidaito.

Shugaban na Sin ya ce, yana da muhimmanci a kara himma wajen ba da fifiko a fannin samar da ci gaba, da zurfafa hadin gwiwar yaki da fatara, da daukar matakan yaki da annobar COVID da samar da rigakafi, a kara bunkasa samar da kudade, da sauya fasalin ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, kana a yi kokarin lalibo sabbin hanyoyin tabbatar da ci gaban duniya, a yi aiki tare gami da bin tsarin hadin gwiwa dake shafar kowane bangare.(Ahmad)