logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbea

2021-12-04 15:37:48 CRI

Shugaban kasar Sin ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbea_fororder_A

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ga taron ministocin kungiyar Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbea ta kafar bidiyo a jiya Jumma’a, inda ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.    

A cewarsa, tarihi ya nuna cewa, neman ci gaba cikin lumana da tabbatar da adalci da daidaito da hadin gwiwar moriyar juna, su ne hanyoyin samun ci gaba. Ya ce Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbea, dukkansu kasashe ne masu tasowa. A cewarsa, kasashen abokai ne dake hulda bisa daidaito da moriyar juna da burin ci gaba na bai daya. Kana burinsu na samun ‘yanci da ci gaba da farfadowa, ya kara musu kusanci.

Bugu da kari, shugaban na Sin ya yi kira ga bangarorin biyu su lalubo hanyoyin inganta dangantakarsu da karfafa ta, tare da bayar da sabuwar gudunmowa ga kyautata zamantakewar jama’arsu da samar musu da ci gaba. (Fa’iza Mustapha)