logo

HAUSA

Hare-hare sun tilastawa sama da ‘yan Nijeriya 11,500 tserewa zuwa Niger a watan Nuwamba

2021-12-04 16:14:26 CRI

Hare-hare sun tilastawa sama da ‘yan Nijeriya 11,500 tserewa zuwa Niger a watan Nuwamba_fororder_RF255154_SayamForage1-0T6A7010

Ofishin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ya ce hare-hare a arewa maso yammacin Nijeriya, sun tilastawa ‘yan kasar sama da 11,500 tsallake iyaka zuwa makwabciyar kasar Nijer a cikin watan Nuwamba, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce kungiyoyi masu dauke da makamai, sun yi ta kai hare-hare kauyukan yankin arewa maso yammacin Nijeriya a makonnin baya-bayan nan, lamarin dake zuwa bayan an samu raguwar rikicin kabilancin tsakanin makiyaya da manoma, yayin da suke fafutukar tara albarkatun dake tabarbarewa, baya kuma ga matsalar sauyin yanayi.

Sanarwar ta ce, hukumar ta damu matuka da karuwar rikici a yankin arewa maso yammacin Nijeriya, don haka take kira da a kara kokarin shawo kan karuwar bukatun jin kai na mutanen da lamarin ya shafa, wandanda suka hada da hidimomin kariya da abinci da matsuguni da kayayyakin girki da barguna da sauran bukatun da ba na abinci ba.

Ta kara da cewa, hukumar da taimakon hukumomin Nijeriyar, na yi wa mutanen dake tserewan rejista da samar musu da taimakon gaggawa da kuma kulawa ta musammam ga mafiya rauni. (Fa’iza Mustapha)