logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gana da Darakta Janar ta WTO

2021-12-04 15:26:01 CRI

Firaministan kasar Sin ya gana da Darakta Janar ta WTO_fororder_A

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da darakta janar ta kungiyar kula da cinikayya ta duniya, Ngozi Okonjo-Iweala, ta kafar bidiyo a jiya Jumma’a.

A cewar Li Keqiang, kasar Sin na goyon bayan kiyaye iko da nagartar ka’idojin WTO, da kiyaye hakkoki da muradun ci gaba na kasashe masu tasowa da rage gibin dake akwai tsakanin manya da kananan kasashe, ta yadda garambawul a kungiyar, zai kasance bisa tafarkin da ya dace.

Li Keqiang, ya kara da cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, Sin za ta nace ga ka’idar tabbatar da daidaiton hakkoki da nauye-nauye, da sauke nauyin dake wuyanta iya karfinta, kuma a shirye take, ta taka rawa cikin yarjeniyoyin kungiyar.

A nata bangaren, Ngozi Okonjo-Iweala, ta yabawa rawar da Sin ke takawa a WTO, ta kuma yaba mata bisa gagarumin gudunmuwar da take bayarwa wajen taimakon kasashen Afrika a fannin yaki da COVID-19 da raya tattalin arzikinsu. Ta ce Sin na da gogewar da kasashe masu tasowa za su iya koyi da su, tana mai fatan karfafa tuntuba da kasar Sin, da kuma hada hannu wajen yi wa WTO garambawul da bada gudunmuwa wajen inganta tsarin cinikayya na duniya. (Fa’iza Mustapha)