logo

HAUSA

Ranar kundin tsarin mulkin kasar Sin: Shugaba Xi ya sha jaddada muhimmancin kundin tsarin mulkin kasar

2021-12-03 14:24:18 CRI

Ranar kundin tsarin mulkin kasar Sin: Shugaba Xi ya sha jaddada muhimmancin kundin tsarin mulkin kasar_fororder_src=http___qqpublic_qpic_cn_qq_public_0_0-1871129092-5AA2CC4045DC5514CC3091E4D22A5EE7_0_fmt=jpg&size=59&h=375&w=782&ppv=1_jpg&refer=http___qqpublic_qpic

Gobe Asabar 4 ga watan Disambar bana, rana ce ta kundin tsarin mulkin kasar Sin karo na 8. Kundin tsarin mulkin kasar Sin, ita ce dokar koli ta kasar, kana babbar ka’ida ce ta tafiyar da harkokin mulkin kasar, wanda ya bayyana niyyar jam’iyyar kwaminis gami da al’ummar kasar Sin. Tun bayan da aka gudanar da babban taro karo na 18 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya zuwa yanzu, shugaba Xi ya sha jaddada muhimmanci gami da martabar kundin tsarin mulkin kasa.

Ya kamata kowane dan kasa ya mutunta kundin tsarin mulki, a matsayin kundin dake kiyaye hakkokin dan Adam. Shugaba Xi ya bayyana cewa, ya dace daukacin al’umma su girmama kundin tsarin mulkin kasa gami da sauran dokokin kasar, su amince da su tare kuma da yin amfani da su yadda ya kamata. (Murtala Zhang)