logo

HAUSA

Li Keqiang ya gana da babbar darektar asusun IMF

2021-12-03 21:07:27 CRI

Li Keqiang ya gana da babbar darektar asusun IMF_fororder_lkq

Da yammacin yau ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da babbar darektan asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Kristalina Georgieva ta kafar bidiyo.

Li Keqiang ya bayyana fatan asusun IMF, zai ci gaba da inganta sauye-sauye a harkokin rabo da tafiyar da mulki, da taka rawar gani wajen taimakawa kasashe masu tasowa, wajen tunkarar annobar COVID-19 da inganta farfadowar tattalin arzikin duniya.

A nata jawabin, Kristalina Georgieva ta yi matukar godiya ga matakai daban-daban da kasar Sin ta dauka, na inganta farfado da bunkasuwar tattalin arziki, tana kuma son kara karfafa mu'amala da hadin gwiwa don sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. (Ibrahim)

Ibrahim