logo

HAUSA

Babban taron MDD na 76 ya amince da kudirin shawarwarin sulhu na gasar Olympics na lokacin sanyi na Beijing

2021-12-03 13:13:37 cri

Babban taron MDD karo na 76 ya amince da kudurin shawarwarin sulhu na gasar Olympic ta birnin Beijing_fororder_0I0102A4-0

A jiya Alhamis ne, aka gudanar da babban taron MDD karo na 76 a birnin New York na kasar Amurka, inda aka amince da kudurin tabbatar da zaman lafiya a lokacin gasar Olympics na lokacin hunturu na birnin Beijing da kasar Sin da kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC) suka tsara.

Kudirin mai taken "Gina zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya ta hanyar wasanni da ruhin gasar Olympic," an amince da shi ne bisa yarjejeniya tare da hadin gwiwar kasashe mambobi 173.

Kudirin ya yi kira da a kiyaye al'adar gudanar da wasannin Olympics da na ajin nakasassu na birnin Beijing na shekarar 2022, kwanaki bakwai gabanin fara gasar wasannin Olympics a ranar 4 ga Fabrairu, 2022 da kuma kwanaki bakwai bayan kammala wasannin nakasassu.

Bugu da kari, kudirin ya yi kira ga daukacin mambobin kasashe, da su hada kai da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa, da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ajin nakasassu na kasa da kasa, a kokarinsu na yin amfani da wasanni a matsayin wani makami na inganta zaman lafiya da tattaunawa da sulhu a yankunan da ake fama da rikici a lokacin gasar wasannin Olympic da na nakasassu da kuma bayan lokacin wasannin Olympics

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC) Thomas Bach ya ce wannan wani babban karramawa ne ga manufar gasar Olympics da ma ajin nakasassu, na hada kan 'yan wasa mafi kyau a duniya wajen yin gasa cikin lumana, da kuma tsayin daka kan duk wata takaddama ta siyasa.(Ibrahim)