logo

HAUSA

Zhang Xiliang: kasar Sin za ta jagoranci aikin daidaita sauyin yanayi bayan shekaru 30

2021-12-03 21:33:09 CRI

Zhang Xiliang: kasar Sin za ta jagoranci aikin daidaita sauyin yanayi bayan shekaru 30_fororder_zhang

An bude taron kasa da kasa game da “Fahimtar Kasar Sin” na shekara ta 2021, mai taken “Daga ina aka fito, ina kuma aka dosa—— Sauye-sauyen duniya na shekaru 100 da kasar Sin, gami da jam’iyyar kwaminis ta kasar” a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, taron da ke gudana daga ranar 1 zuwa 4 ga watan nan.

A zantawarsa da wakilin CMG Zhang Xiliang, shugaban cibiyar nazarin makamashi, muhalli da tattalin arziki na jami’ar Tsinghua, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kafa sabon tsarin makamashi, bayan shekaru 30 inda sabbin makamashi za su taka babbar rawa. A lokacin ne kuma, za ta fitar da abubuwa masu gurbata muhalli kadan. Kuma ingancin iska zai kai mazanin WHO. Haka kuma kasar Sin za ta jagoranci aikin daidaita sauyin yanayi a duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan