logo

HAUSA

Shugaban kungiyar nazarin kayan tarihin kasar Sin: Ya dace a yi amfani da kayan tarihi don bayyana labaran kasar Sin

2021-12-03 12:57:01 CRI

Shugaban kungiyar nazarin kayan tarihin kasar Sin: Ya dace a yi amfani da kayan tarihi don bayyana labaran kasar Sin_fororder_A

Daga ranar 1 zuwa 4 ga watan nan, a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, an yi taron kasa da kasa mai suna “Fahimtar Kasar Sin” na shekara ta 2021, mai taken “Daga ina ta fito, ina kuma ta dosa—— Sauye-sauyen duniya na shekaru 100 da kasar Sin, gami da jam’iyyar kwaminis ta kasar”.

A zantawarsa da wakilin CMG, wato babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, tsohon shugaban gidan adana kayan tarihi dake fadar sarakunan gargajiya na kasar, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar nazarin kayan tarihin kasar Sin, Mista Shan Jixiang ya ce, wata hanya ta musamman da gidan adana kayan tarihin fadar sarakunan gargajiyar kasar Sin ke bi wajen yada labarai, ita ce, nuna himma da kwazo wajen shirya bukukuwan nune-nune.

Kaza lika a kan shirya bukukuwa da dama a kasashe masu mabambantan tsare-tsaren siyasa a duk fadin duniya, a wani kokari na bayyana al’adun gargajiya, gami da irin kokarin da kasar Sin take yi wajen kiyaye al’adun gargajiyarta. (Murtala Zhang)