logo

HAUSA

An yi taron kasa da kasa mai taken “Fahimtar Kasar Sin” a Guangzhou

2021-12-03 12:51:09 CRI

An yi taron kasa da kasa mai taken “Fahimtar Kasar Sin” a Guangzhou_fororder_1128125452_16384503690331n

Jiya Alhamis ne aka bude taron kasa da kasa da aka kira “Fahimtar Kasar Sin” na shekara ta 2021 a birnin Guangzhou dake kudancin kasar, inda memban ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar, Mista Huang Kunming ya halarci bikin bude taron, gami da gabatar da muhimmin jawabi ta kafar bidiyo.

Mista Huang ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping yana matukar maida hankali kan wannan taro, inda ya gabatar da jawabi na musamman ta kafar bidiyo, wanda cikin sa ya yaba da muhimmiyar rawar da taron ya taka tun farkon kafuwarsa zuwa yanzu, da bayyana babbar ma’anar jajircewar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi na tsawon shekaru 100 ga ci gaban duk fadin duniya, da shaida babbar niyyar jam’iyyar na kara biyan bukatun al’umma a fannin jin dadin rayuwa, da kuma samar da karin gudummawa ga duniya, al’amarin da ya kafa alkibla ga gudanar da taron, da kara fahimtar kasar Sin yadda ya kamata. (Murtala Zhang)