logo

HAUSA

An cafke wani mutum da ya rika sintiri dauke da bindiga a kusa da helkwatar MDD na birnin New York

2021-12-03 10:55:45 cri

An cafke wani mutum da ya rika sintiri dauke da bindiga a kusa da helkwatar MDD na birnin New York_fororder_0ab46f61d68a4d4690d06119e5bf02a2

A jiya Alhamis, ‘yan sanda a birnin New York, sun damke wani mutum da ya rika sintiri dauke da bindiga a kusa da helkwatar MDD, bayan shafe sa’o’i 2 da rabi ana kika kaka tsakanin sa da jami’an tsaro.

Majiyar jami’an tsaro, ta ce mutumin wanda ke dauke da bindiga da kuma wani kundin takardu, ya rika kai-komo a titunan dake daura da ginin MDDr, tun daga karfe 11:15 na safe, wanda hakan ya sa jami’an tsaro suka killace wasu sassan yankin da ginin yake, zuwa karfe 1 da ‘yan mintuna, lokacin da mutumin ya amince ta mika kan sa.

An ce ‘yan sanda sun karbi kundin takardun da yake tare da su, suka kuma mika su cikin ginin MDD, kana suka sanya masa ankwa, tare da tusa keyarsa cikin wata motar daukar marasa lafiya. To sai dai kuma ba a kai ga bayyana abubuwan da takardun da ya gabatar suka kunsa ba.

Daga bisa sani, da misalin 1:55 na rana, jami’an MDD sun ce ‘yan sanda sun kai ga shawo kan wannan al’amari, kana an bukaci daukacin ma’aikatan dake aiki a helkwatar MDDr da su koma bakin aikin su ba tare da wata fargaba ba.  (Saminu)