logo

HAUSA

Zhao Ai: raya hanyar siliki ba tare da gurbata muhalli ba, wata hanya ce mai dacewa wajen bayyana labarun kasar Sin da kyau

2021-12-03 21:34:45 CRI

Zhao Ai: raya hanyar siliki ba tare da gurbata muhalli ba, wata hanya ce mai dacewa wajen bayyana labarun kasar Sin da kyau_fororder_zhao

An bude taron kasa da kasa game da “Fahimtar Kasar Sin” na shekara ta 2021, mai taken “Daga ina aka fito, ina kuma aka dosa—— Sauye-sauyen duniya a shekaru 100 da kasar Sin, gami da jam’iyyar kwaminis ta kasar” a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, taron da ke gudana daga ranar 1 zuwa 4 ga watan nan.

Zhao Ai, mataimakin shugaba kuma babban darektan cibiyar nazarin yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar Sin, kuma tsohon jami’in kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya zanta da wakilin CMG, inda ya nuna cewa, wajibi ne a raya hanyar siliki ba tare da gurbata muhalli ba cikin hadin gwiwar sassa daban daban, a fannonin daidaita sauyin yanayi, rage radadin bala’u daga indallahi, kiyaye muhalli da rage talauci. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan