logo

HAUSA

Sin ta samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 1.85 ga kasashen duniya

2021-12-03 20:29:49 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labarun da aka gudanar a yau cewa, Sin ke kan gaba wajen samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 ga kasashen duniya, inda ta samar sama da allurai biliyan 1.85.

Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana a kwanakin baya cewa, ya zuwa yanzu, babu wata kasa mai karamin karfi a duniya ta cimma burin yiwa kashi 40 cikin 100 na al’ummar alluran rigakafin cutar COVID-19, watakila ba za a cimma burin MDD na yiwa kashi 40 cikin dari na al’ummar duniya rigakafi kafin karshen shekarar 2021 ba.

Zhao Lijian ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 masu inganci ga kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga rarraba alluran da yin amfani da su cikin adalci a duniya, da ci gaba da samar da gudummawa wajen cimma nasarar yaki da cutar COVID-19 cikin hanzari. (Zainab)