logo

HAUSA

An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na hadin gwiwar Sin da Amurka game da sauyin yanayi cikin nasara

2021-12-03 13:21:56 cri

An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na hadin gwiwar Sin da Amurka game da sauyin yanayi cikin nasara_fororder_11111111

A jiya Alhamis ne aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki, na hadin gwiwar Sin da Amurka game da sauyin yanayi cikin nasara. Taron mai taken "Hadin gwiwar kawo sauyi game da sauyin yanayi na Sin da Amurka " ya gudana ne a gefen taron kasa da kasa mai lakabin “Fahimtar Kasar Sin” na shekarar 2021, wanda ya gudana a birnin Guangzhou na kasar Sin.

Taron ya kuma samu halartar manyan tsofaffin jagorori, da shugabanni, da kwararru daban daban, da kuma manyan malamai a fannin sauyin yanayi daga sassan kasar Sin.

Bakin sun kuma amince da cewa, a yanzu haka kullum ana fuskantar matsalolin sauyin yanayi. Don haka Sin da Amurka na da nauyin yin hadin gwiwar shawo kan kalubalen da duniya ke fuskanta game da sauyin yanayi a matsayinsu na manyan kasashe.     (Saminu)