logo

HAUSA

Kafar CGTN da wasu manyan kafofin watsa labaran kasashen Latin Amurka sun bullo da shawarwari game da matakan da za su dauka cikin hadin-gwiwa

2021-12-03 10:49:50 CRI

Kafar CGTN da wasu manyan kafofin watsa labaran kasashen Latin Amurka sun bullo da shawarwari game da matakan da za su dauka cikin hadin-gwiwa_fororder_A

A yayin da ake shirye-shiryen taron ministoci karo na uku, na dandalin tattaunawa tsakanin kasar Sin da gamayyar kasashen nahiyar Latin Amurka, a jiya Alhamis, kafar CGTN dake karkashin babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ta hada kai tare da wasu manyan kafofin yada labarai sama da 30 na kasashen nahiyar Latin Amurka, don bullo da shawarwari game da matakan da za su dauka cikin hadin-gwiwa.

Dandalin kafafen yada labaran Sin da kasashen Latin Amurka, zai zurfafa hadin-gwiwa, da kara samun fahimtar juna tsakanin kafafen yada labarai daban-daban ta hanyoyi da dama, ciki har da shirya dandalin tattaunawa ta kafar intanet, da daukar shirye-shiryen bidiyo tare, da nuna fina-finai da sauransu.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaba, kana babban editan CMG Mista Shen Haixiong, ya gabatar da wani muhimmin jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce, a cikin jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a gun bikin bude taron kolin shugabannin kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen nahiyar Latin Amurka wanda aka shirya a shekara ta 2016, ya ce mu’amalar kafafen yada labarai muhimmin sashi ne a alakokin Sin da Latin Amurka. Ita dai kafar CMG ta dade tana jajircewa wajen inganta hadin-gwiwa da cudanya tsakanin kafafen yada labaran Sin da na Latin Amurka, don kara samun fahimtar juna da yin koyi daga juna. A nan gaba ma, CMG za ta ci gaba da tsayawa haikan, wajen yin mu’amala da kafofin yada labaran kasashen Latin Amurka, da fadada hanyoyin yin hadin-gwiwa, a wani kokari na taimakawa ci gaban alakokin Sin da Latin Amurka. (Murtala Zhang)