logo

HAUSA

An wallafa jerin litattafai masu taken “Fahimtar kasar Sin” karo na biyu

2021-12-02 15:47:25 CRI

An wallafa jerin litattafai masu taken “Fahimtar kasar Sin” karo na biyu_fororder_11

A ranar 1 ga wata, an yi bikin wallafa jerin litattafai masu taken “Fahimtar kasar Sin” karo na biyu a hukumance a birnin Guangzhou na kasar Sin.

A yayin bikin, shugaban kungiyar nazarin manufofin kirkire-kirkire da ci gaban kasa ta kasar Sin, Zheng Bijian ya ce, kasar Sin ba ta daina aikin neman ci gaba da yin kwaskwarima ba, za ta kuma ci gaba da aikin “Fahimtar kasar Sin”, da fatan gamayyar kasa da kasa za su fahimci da girmama tarihi, da fatan al’ummomin kasar Sin.

An wallafa jerin litattafai masu taken “Fahimtar kasar Sin” karo na biyu_fororder_12

Kaza lika, marubucin kasar Indonesiya Jusuf Wanandi ya ce, “Litattafan da aka wallafa a karo na farko, sun burge ni sosai, na amince da ra’ayoyi da ilmmoin da aka rubuta a cikinsu, sun kara min sani game da kasar Sin.”

An wallafa jerin litattafai masu taken “Fahimtar kasar Sin” da harsuna da dama. A shekarar 2018, aka wallafa litattafan a karo na farko, ciki har da litattafai sama da 40 na Sinanci, na Turanci, da kuma na Japannanci. Haka kuma, an fassara su zuwa harsuna daban daban, domin wallafa a kasashen ketare. (Maryam)