logo

HAUSA

Zhang Yi: JKS tana tsayawa tsayin daka kan burin neman ci gaba

2021-12-02 15:49:54 CRI

Zhang Yi: JKS tana tsayawa tsayin daka kan burin neman ci gaba_fororder_31

A ranar 1 ga wata, aka kaddamar da taron “Fahimtar kasar Sin” na shekarar 2021 a birnin Guangzhou na kasar Sin.

A yayin taron, shugaban kwalejin nazarin manufofin raya zamantakewar al’umma na cibiyar koyon ilmin zamantakewar al’umma ta kasar Sin, Zhang Yi ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin ta samar da damammaki ga kasa da kasa, bunkasuwar kasashen duniya ta kuma samar da damammaki ga kasar Sin. Ya kamata mu hada su tare, domin samun karuwar tattalin arziki cikin saurin gaske, da kuma tabbatar da zaman karko a zamantakewar al’umma cikin dogon lokaci. (Maryam)