logo

HAUSA

Shugaban Afirka ta kudu ya ziyarci Najeriya duk da tsoron da ake yi na bazuwar nau’in COVID-19 na Omicron

2021-12-02 09:40:46 CRI

Shugaban Afirka ta kudu ya ziyarci Najeriya duk da tsoron da ake yi na bazuwar nau’in COVID-19 na Omicron_fororder_Buhari

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana ziyarar da takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya yi a Najeriya a matsayin mai cike da nasara, duk da damuwar da aka rika nunawa game da bazuwar sabon nau’in cutar COVID-19 na Omicron.

Yayin taron manema labarai da shugabannin biyu suka halarta a birnin Abuja, shugaba Buhari ya ce sun sanya hannu kan wasu yarjeniyoyin fahimtar juna a madadin kasashen su, wadanda suka jibanci sassa da dama, sun kuma yi nazari kan yarjeniyoyin da tuni aka amince da su, domin cin gajiyar al’ummun kasashen biyu.

Shugaban Najeriyar ya ce "Mun kai ga kawo karshen dukkanin ziyarce ziyarce da muka tsara cikin nasara, mun kuma kammala taruka 10 karkashin dandalin hadin gwiwar Najeriya da Afirka ta kudu. Duk da bullar sabon nau’in cutar COVID-19, mun yi nasarar gudanar da tattaunawa cikin nasara, tare da kiyaye matakan kare lafiya bisa hadin kai da fahimtar juna".

Jami’an kasashen biyu dai sun sanya hannu kan yarjeniyoyin fahimtar juna a fannonin bunkasa ci gaban matasa, da mata da yara kanana. Sai kuma fannonin tuntuba a bangaren siyasa, da karin muhimman sassa na  musaya tsakanin al’ummun Najeriya da na Afirka ta kudu.  (Saminu)